Yanzu-Yanzu: An gudanar da gagarumin zanga-zanga a birnin Minna

Matasan yankin Kpakungun da ke Minna, a ranar Litinin, 31 ga watan Agusta, sun toshe manyan hanyoyin Minna, babbar birnin jihar Neja domin zanga-zanga a kan rashin wutar lantarki a birnin.

Fusatattun matasan sun kuma kora babban sakataren gwamnatin jihar Neja, Alhaji Ahmed Matane, wanda ya roke su a kan su bude manyan hanyoyin da kuma dakatar da zanga-zangar.

Matasan sun kaddamar da cewar sun gaji da gurguntaccen wutar lantarki da ake basu, cewa kamfanin wuta na Abuja (AEDC) ta wofantar da al’umma. Hanyar Kpakungun shine hanya guda da ke sada mutane da yankunan kudancin kasar kuma ya kasance daya daga cikin manyan hanyoyin da aka fi amfani da su a jihar.

Masu mota musamman wadanda ke tafiya kudu sun yi cirko-cirko a hanyar, jaridar The Nation ta ruwaito. Duk kokari da gwamnatin jihar ta yi na ganin masu zanga-zangar sun kawo karshen shirin ya ci tura yayinda SSG ya yi gaggawan barin wajen bayan ihun da aka masa.

Daya daga cikin kansilolin da ke wakiltan unguwar Minna ta Kudu, Aminu Ladan, ya fada wa masu kawo rahoto cewa babu wani bayani daga hukumomi, cewa zanga-zangar ya gudana cikin lumana.

“Kamar yadda kuke gani, an kori SSG cikin fushi kuma bai yi nasarar isar da sakon da ya kawo ba. Mutanena na son gwamna ya bayyana. “A matsayina na wanda ke rike da mukamin siyasa, na san cewa SSG wakilin Gwamna ne amma mutanen basu fahimci haka ba.

Basu gamsu ba kuma suna son Gwamna ya zo da kansa,” in ji shi. Matasan sun sha alwashin rufe hanyar na tsawon sa’o’i 24 har sai gwamnan ya bayyana.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt


Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN