• Labaran yau


  Dattawan Arewacin Najeriya sun juya wa majalisar dokoki baya, duba dalili

  Kungiyar dattawan arewacin Najeriya ta yi watsi da wata gayyata da wani kwamitin wucin gadi na majalisar dattawa ya yi wa jama'ar kasar domin su bayyana ra'ayinsu game da shirin gyaran kundin tsarin mulkin Najeriyar. 


  Kungyar ta Northern Elders Forum, wadda Farfesa Ango Abdullahi ke jagoranta, ta ce majalisar na so ne kawai ta bata lkacin 'yan kasar ba tare da ta aiwatar da abubuwan da suka kamata ba. 


  Kungiyar dattawan arewar, wadda ta yi kira ga sauran kungiyoyin farar hula na yankin da su kauracewa gayyatar da majalisar dattawan ta yi, ta ce a ganinta duk wani shirin gyaran kundin tsarin mulki da za a yi bata lokaci da kudade ne kawai. 


  Dokta Hakeem Baba-Ahmed, daraktan yada labarai na kungiyar ta Northern Elders Forum, ya yi wa AbdusSalam Ibrahim Ahmed karin bayani.

  Source: BBC
   

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Dattawan Arewacin Najeriya sun juya wa majalisar dokoki baya, duba dalili Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama