• Labaran yau


  Malamin Islamiyya ya yi wa yar shekar 15 fyade da sunan zai taimaketa ta cire cikin shege

  Rundunar yansandan jihar Ogun ta kama wani Malamin Islamiyya dan shekara 38 mai suna Ismaila Saheed da Toliha Sabith mai shekara 20 bisa zargin yi wa karamar yarinya mai shekara fyade 15.

  Rahotun yansanda ya ce Sabith ne ya fara yi wa yarinyar fyade a unguwar Imedu-nla da ke garin Mowe. Daga bisani yarinyar ta kai kara wajen Malamin Islamiyya wanda shi kuma ya yi amfani da wannan dama ya yi mata fyade da sunan zai taimaketa domin a cire cikin gaba da fatiha da ta dauka bayan saduwar farko da Sabith.

  Bayan yarinyar ta shigar da kara wajen yansanda, DPO Bala Yakubu, ya umarci yansanda masu bincike su kamo Malamin tare da Sabith, wanda suka amsa laifinsu yayin binciken yansanda. An mika mutanen zuwa sashen bincike na SCIID domin fadada bincike kan lamarin.  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Malamin Islamiyya ya yi wa yar shekar 15 fyade da sunan zai taimaketa ta cire cikin shege Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama