• Labaran yau


  Katon rami ya rufta a tsakiyar hanyar Kaduna zuwa Zaria (Hotuna)


  Hukumoni a ranar Litinin sun rufe hannu daya na babbar hanyar Kaduna zuwa Zaria, wacce ke kusa da ginin kasuwar duniya ta Kaduna, bayan wani katon rami ya bayyana kusa da gadar da ke kan hanyar.


  Jaridar Daily Trust ta gano cewa, lamarin ya faru ne bayan cunkoson kan titin na ranar Lahadi tare da ruwa mai karfi da aka yi na sama ya kawo fadawar wani katon rami Babu wanda ya rasa ransa a yayin da lamarin ya faru, ganau ba jiyau ba ya sanar da hakan.


  A ranar Litinin, an gano cewa hanya daya ce ke aiki inda jami'an tsaro suka garkame dayar. Jami'an kiyaye hadurran kan titi na tarayya (FRSC) ne suke bai wa masu ababen hawa hannu don sauya hanya.


  Wani dan achaba mai suna Suleiman Umar, wanda ya zanta da manema labarai, ya ce an sanar da shi cewa ramin ya rufta bayan da wasu manyan motocin siminti biyu suka wuce ta kan gadar.Masu achaba kuwa sun ci gaba da amfani da hanyar da ramin yake amma ta gefen da abun bai shafa.


  Source: Legit


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Katon rami ya rufta a tsakiyar hanyar Kaduna zuwa Zaria (Hotuna) Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama