• Labaran yau


  Kalli bidiyon fashewar wani abu da ya raunata daruruwan jama'a a birnin Beirut

  An sami fashewar wani abu mai karfin gaske da ya razana jama'a a birnin Beirut na kasar Lebanon ranar Talata 4 ga watan Agusta.

  Fashewar da ya auku da tsakar rana ya haddasa barna mai yawa ga dukiyan jama'a tare da raunata daruruwan mutane kamar yadda kungiyar Red Cross a garin ta sanar.

  Gidan Talabijin na yankin ya labarta cewa  fashewar ya auku ne a tashar ruwa na Beirut a cikin wajen da ake ajiye kayan fashe-fashe na bukukuwa.

  Wani dan Jarida da ke wa AP aiki ya ce ya gani da idonsa yadda jama'a da dama suka sami raunuka a yankin da lamarin ya faru a tsakiyar birnin Beirut.

  Latsa kasa ka kalli bidiyo fashewar:  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kalli bidiyon fashewar wani abu da ya raunata daruruwan jama'a a birnin Beirut Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama