Kwamishinan Ƙananan Hukumomi na jihar Kano, Murtala Sule Garo yana fuskantar tuhuma daga Hukumar Hukunta Masu Yi wa Tattalin ArziÆ™in Ƙasa Ta’annati, EFCC bisa zargin sa da mallakar wasu gidaje a Kano da Abuja.
Mista Garo yana ɗaya daga cikin manyan kwamishinoni a ƙunshin kwamishinonin Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje.
Mai Magana da Yawun EFCC, Dele Oyewale, ya tabbatar wa da jaridar Intanet, Daily Nigerian cewa sun “gayyaci kwamishinan ne kawai, ba kamawa ba”, don ya yi bayanin “abu É—aya ko biyu”.
Sai dai wasu majiyoyi sun shaida wa Daily Nigerian cewa ofishin EFCC na Kano ya gayyaci Mista Garo ne don ya yi bayanin inda ya samu tarin dukiyarsa da ta haÉ—a da rukunin gidaje, gidajen mai da sauransu.
Source: alummata
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/