Gwamna Ganduje Ya Nada Sabon ‘Pro-Chancellor’ Na Jami’ar Yusuf Maitama Sule

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya naɗa Shugaban Jami’ar Bayero ta Kano, BUK, Farfesa Yahuza Bello Pro-chancellor na Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta Kano, YUMSUK.
Gwamna Ganduje ya bayyana Litinin cewa wannan naɗi ya fara aiki ne nan take, kamar yadda jaridar Intanet, Kano Focus ta rawaito.
Mista Bello, Farfesan Lissafi, ya taɓa riƙe Shugaban Sashin Kimiyyar Lissafi daga 1991 zuwa 1999, Shugaban Tsangayar Kimiyya, daga 1995 zuwa 1995, kuma Daraktan Sashin Fasahar Yaɗa Labarai, daga 2003 zuwa 2007, Shugaban Makarantar Karatun Gaba Da Digirin Farko daga 2009 zuwa 2010, kuma Mataimakin Shugaban Jami’a mai kula da Ɓangaren Karatu har sau biyu duk a Jami’ar Bayero ta Kano, BUK.
Tsohon Pro-chancellor na YUMSUK, Sule Yahaya Hamma ya yi murabus daga muƙamin nasa ranar 12 ga Yuni, yana mai kafa hujja da dalilan ƙashin kai.
Source: alummata

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN