Ko me ke kawo larurar galhanga ga yara?

Larurar galhanga wacce ake cewa "Autism Spectrum Disorder" a turance, larura ce da aka yi mata gurguwar fahimta a cikin al'umma, inda ake ganin masu larurar a matsayin masu
raunin hankali ko ma taɓin hankali.




Galhanga larura ce da ke shafar ci gaban ƙwaƙwalwa da ke da tasiri kawo cikas wajen hulda da kuma sadarwa ga mai larurar.

Galhanga na fara nuna alamu tun a yarinta wanda daga baya kuma matsalolin hulda da zamantakewa su biyo baya. Sau tari, yara masu galhanga na fara nuna alamu tun a shekarar farko. Amma kaÉ—an daga cikin yaran ba sa nuna alamu a shekarar farko sai bayan sun fara girma sai kuma ci gaban girmansu ya fara komawa baya tsakanin watanni 18 zuwa watanni 24 inda alamun galhanga za su fara bayyana.


Alamomin larurar galhanga

Wasu yaran na nuna alamun galhanga tun suna yara ƙanana, wasu kuma har sai sun fara tasawa. Amma alamun sun fi bayyana a shekarar yaro ta biyu. Kuma kowanne yaro mai galhanga na nuna alamu da suka sha bam-bam da na wani. Amma yawancinsu suna nuna wasu alamu da ɗabi'u bai-ɗaya.


Alamun sun haÉ—a da:

1. Ƙin yarda su haɗa ido da iyaye, mutanen gida ko mai raino.
2. Gaza gane sunansu yayin da aka kira sunansu.
3. Matsananciyar ɗafa yayin da aka yi ƙoƙarin ɗaukansu ko saka su a jiki. Saboda haka, sun fi son su kasance su kaɗai ko da yaushe.
4. Gaza bayyanar dariya, murmushi ko É“acin rai a fuskarsu.
5. Gaza magana/furuci, ko kuma jinkirin fara maganar. Wani lokacin kuma su mance da kalmomi ko jimlolin da suka fara iya furtawa a baya.
6. Gaza farar da hira, ko ambatar sunan wani abu da suka gani ko suka hanga.
7. Maimaita kalmomi ko gajerun jimlolin yayin da suka ji wani ya faÉ—a, amma ba su san yadda za su yi amfani da su a cikin zance ba.
8. Wahalar gane umarni, kwatance ko tambaya.
9. Ba sa iya nuna abu ko nuna sha'awarsu kan wani abu, misali, kayan wasan yara kamar 'yar tsana da sauransu.
10. Saurin fushi, kuka ko bore kan ƙanƙanin abu, dai da sauransu.
11. Jinkiri ko wahalar koyon karatu a makaranta. Amma wasu masu larurar kan zo da kaifin basira mai ban mamaki, musamman a É“angaren lissafi.
Sabuban larurar galhanga


Har zuwa yanzu, ba a san takamaiman sababin larurar galhanga ba. Sai dai, masana na alaƙanta sababin da jirkicewar jigidar halitta (genetic mutation) da kuma wasu ƙalubalen muhalli, kamar shan magungunan kashe ƙwayoyin cuta, matsalolin rainon ciki, da kuma gurɓatacewar iska da sauransu.
Matsalolin da ke kawo haifar yaro mai galhanga.


Larurar galhanga na iya faruwa ga yara a kowanne jinsi ko ƙasa. Amma akwai wasu abubuwa da ke ƙara haɗarin haifar yaro mai galhanga kamar haka:

1. Yara maza sun fi yara mata haÉ—arin samun galhanga da ninki huÉ—u.
2. Samun galhanga guda a iyali/dangi na ƙara haɗarin samun wani yaron mai galhanga.
3. Haihuwar bakwaini ko yaran da aka haifa kafin ciki ya cika makonni 26.
Ƙalubalen da mai larurar galhanga ke fuskanta

Ƙalubalen da masu galhanga ke fuskanta na zamantakewa, sadarwa, da baƙin ɗabi'u na kawo musu cikas wajen:

1. Matsalar koyon karatu a makaranta.
2. Gaza kula da kansu.
3. Ƙaurace wa mutane ko ware kai daga mutane, da sauransu.
Daga ƙarshe, ya kamata mutane su fahimci cewa irin waɗannan yara masu galhanga ba masu taɓin hankali/ƙwaƙwalwa ba ne, face dai suna da buƙata ta musamman. Haka nan, akwai likitoci da ke kula da matsalar harshe/furuci wato "speech therapists/speech and language pathologist", da kuma malamai da ke koya wa masu buƙata ta musamman karatu domin su sami ilmi kamar sauran lafiyayyun yara.

Bugu da ƙari, yara masu larurar galhanga su kan zo da matsalar jinkirin matakan girmansu. Saboda haka, su kan gaza iya riƙe wuya, zama, tsaiwa ko tafiya a watannin da ya kamata su cimma waɗannan matakai.


Tintiɓi likitan fisiyo idan yaro mai galhanga na fama da matsalolin da aka ambata.
\
Source: Physio Hausa


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt


Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN