Duba matsaloli da illoli da ke tattare da cin daskararre ko sarrafaffen mai ga lafiyar ka

Mai ko kitse na daga cikin ajujuwan abinci da jiki ke buƙata. Sai dai, daga cikin ajin mai ko kitse akwai mayuka mafi haɗari ga lafiyar zuciya.

Na farko, akwai daskararren mai, wato 'saturated fat' a turance. Daskararren mai shi ne duk wani irin mai da ke daskarewa ko ya yi bacci haka kawai yayin da aka ajiye shi.

Misalin abincin da ke danƙare da daskararren mai sun haɗa da: kakide ko kitse, naman shanu, jan nama, madarar shanu, man shanu, cuku ko cukwi, man kwakwar manja, manja da sauransu.

Na biyu, sarrafaffen mai, wato 'trans fat' a turance. Nau'in mai ne da masana'antu ke sarrafa shi bayan cakuÉ—a tsinkakken mai, kamar man gyaÉ—a ko man zaitun, da sinadarin haidirojin (hydrogen) domin samar da sarrafaffe kuma daskararren mai.

Masana'antu da wuraren samar da abinci suna amfani da wannan sarrafaffen mai domin ya fi jure zafi, saboda haka, zai daɗe ana amfani da shi ba tare da ya ƙone ba.

Bugu da ƙari, sarrafaffen mai yana ƙara wa abinci ɗanɗano kuma yana sa abincin ya daɗe bai lalace ba. Kuma sarrafaffen mai shi ne nau'in man da ake amfani da shi wajen yin sarrafaffun abinci ko kuma yin sinadari da shi.

Misalin abincin da ake amfani da sarrafaffen mai ko kuma yin sinadari da shi sun haÉ—a da: 'doughnuts', 'cakes', 'pie crusts', 'biscuits', 'porpcorn', 'frozen pizza', 'cookies', 'crackers', da 'margarines' wato bota in ji Bahaushe, da dai sauransu.

Da fatan za ku gafarce mu saboda gaza faÉ—ar waÉ—annan abinci a harshen Hausa, hakan ya faru ne saboda daman ba abincin malam Bahaushe ba ne, amma hotunan da muka saka a nan za su taimaka wajen gane wasu daga ciki.

A dunƙule, daskararren mai da sarrafaffen mai sune mayuka mafiya haɗari ga lafiyar zuciya. Saboda waɗannan mayuka sune suke yawaita kwalastirol (cholesterol) mara kyau, sannan su ƙaranta kwalastirol mai kyau a cikin jini.

Kwalastirol mai kyau shi ne yake yashe ko wanke kwalastirol mara kyau daga cikin jini. Shi kuwa kwalastirol mara kyau shi ne yake kwanciya a cikin jijiyar jini yau da gobe har ya toshe ta.

A yayin da kwalastirol mara kyau ya toshe jijiyar jini zai haifar da bugun zuciya da kuma matsalolin tsohewar jijiyar jini a sauran sassan jiki.

Daga ƙarshe, Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce abincin da ke ɗauke da sarrafafen mai yana ƙara haɗarin ciwon zuciya da kusan kaso 30 cikin 100 (30%).

Fara rage daskararre da sarrafaffen mai a yau don lafiyar zuciyarka.

Source: Physio Hausa

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN