Mutum fiye da 1, 000 aka kashe a Kauyukan Arewa a cikin watanni 6 – Kungiya

Kungiyar Amnesty International ta Najeriya ta ce sama da mutane 1, 000 aka kashe a Arewacin Najeriya a watanni shida da su ka wuce.
Wannan kungiya mai kare hakkin Bil Adama ta ce kauyawa akalla 1, 126 su ka rasa rayukansu a hannun ‘yan bindiga a tsakanin wannan lokaci.
Amnesty International ta ce miyagun ‘yan bindiga sun yi wannan ta’adi ne a jihohin Kaduna, Katsina, Neja, Filato, Sokoto, Taraba da jihar Zamfara.
An yi wannan kashe-kashe ne tsakanin watan Junairu zuwa Yuni a shekarar 2020 kamar yadda kungiyar ta bayyana a wani jawabi da ta fita.
Amnesty ta ce ta tattauna da wadanda rikicin ya shafa da kuma wadanda su ka shaida lamarin, wadanda su ka tabbatar da sakacin jami’an tsaro.
Mutanen kauyukan da aka kai wa hari sun shaidawa kungiyar cewa jami’an tsaro su na kawo masu dauki ne tsawon lokaci bayan an kai masu harin.
Kauyawan da ake yi wa kisan gilla sun bayyana rashin daukar matakin hukunta masu laifi a matsayin abin da ya ke kara hura wutar wannan kashe-kashe.
A cewar kungiyar, manoma da masu kare hakkin jama’a da sauran ‘yan gwagwarmaya su na fuskantar barazana wajen kiran gwamnati ta tashi tsaye.
Darektan Amnesty International na kasar nan, Osai Ojigho, ya ce abin kunya ne ace jami’an tsaro da hukumomin kasar sun gaza kare rayukan mutanen kauye.
Osai Ojigho ya ke cewa ‘yan bindiga su kan shiga garuruwa a kan babura, su na harbin Bayin Allah, sannan su sace dabbobi, su kona gidaje, su yi garkuwa da mutane.
An sace mutum 380 a Kaduna, Neja, Katsina, Nasarawa da Zamfara a bana, kungiyar ta ce mata aka fi sacewa. Sannan akwai mutane 31, 00 da aka raba da gidajensu a Katsina.
Lamarin ya fi kamari a Kaduna inda aka rasa mutane 366 a wata shida. A Taraba rikicin kabilanci ya ci mutane 77, yayin da aka kashe mutane fiye da 70 a Sokoto.
Source: Legit

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN