Rahotanni daga Abuja na cewa an canjawa dan jaridar gidan talabijin na Channelstv wajan aiki daga fadar shugaban kasa zuwa majalisa saboda bidiyon sirri da ya dauka da ya nuna tsohon shugaban APC, Adams Oshiomhole da shugaban Ma’aikatan fadar shugaban, Farfesa Ibrahim Gambari suna maganar kama wasu.
Bidiyon ya watsu sosai a shafukan sada zumunta inda aka gansu suna magana yayin da suke tafiya a cikin fadar. Hutudole ya ruwaito muku cewa PDP ta yi Allah wadai da wannan lamari inda ta yi kiran cewa a binciki manyan mutanen 2.
Saidai daga baya fadar shugaban kasar tace mutanen 2 masu kima ne da bazasu bari a yi wani abu da zai tozarta wani ba.
Hutudole
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/