Targaɗe rauni ne ga tantani ko tantanai da ke riƙe da ƙashi da ƙashi a gaɓa. Wannan rauni kan kasance sakamakon faɗuwa, tintiɓe, tsalle, bugu, murɗewar ko ɗamewar gaɓa fiye da ƙima, da sauransu. Haka nan, targaɗe yana faruwa a kan gaɓa ne kawai.
Matakan targaɗe: An kasa matakin targaɗe zuwa matakai uku kamar haka:
1] Matakin farko: Tantanin zai sami rauni saboda ɗamewa.
2] Mataki na biyu: Tantanin zai sami rauni saboda 'yar yagewa ko tsagewa.
3] Mataki na uku: Tantanin zai tsinke ne gaba ɗaya.
Alamun targaɗe sun haɗa da faruwar waɗannan abubuwa a gaɓar:
1] Ciwo
2] Kumburi
3] Ɗumi idan aka taɓa gaɓar
4] Kasa iya aiki da gaɓar
Abin da ya kamata a yi bayan targaɗe:
1] A kare gaɓar ta yadda ba za a ƙara yin irin motsin da ya haddasa ciwon ba.
2] A hutar da gaɓar da ta samu targaɗen daga aikinta, saboda ci gaba da aikinta na iya ta'azzara raunin, misali, za a iya hutar da gaɓar ta hanyar amfani da kwara-kwara ko kwagiri yayin tafiya.
3] A sanya ƙanƙara a wurin ƙimanin mintina 15 zuwa 20: Za a sami ƙanƙara sai a faffasata, sannan a ɗaure ta a zani ko tawul mai tsabta, sai a sanya ta a daidai raunin har sai ta yi kimanin mintina 15 zuwa 20 sannan a cire daga kan targaɗen.
4] A naɗe ko a ɗaure da bandeji; wannan zai temaka wajen kare gaɓar da kuma rage kumburi.
5] A ɗaga gaɓar da ta yi targaɗen sama; misali, ta hanyar ɗora ta a kan filo yayin da ake kwance.
6) Bayan wannan taimakon gaggawa, sai a gaggauta tintiɓar likitan fisiyo domin dubawa da kuma ci gaba da jinyar targaɗen har ya warke kuma gaɓar ta dawo aiki yadda ya kamata.
Warkewa ta wannan hanya zai sa tantanan su warke, sannan a magance motsawar raunin ko tashinsa ta hanyoyi da dama kamar; amfani da na'urorin rage raɗaɗi da kuma na'urorin da ke haɓaka tohowar tantani ba tare da dogara kan shan magunguna ba.
Abubuwan da ba a son yi bayan targaɗe:
1) Kada a lallanƙwasa ko mimmiƙar da gaɓar da zarar an yi targaɗe da zimmar dawo da aikin gaɓar ko rage raɗaɗin ciwo.
2) Kada a mulmula wurin targaɗen.
3) Kada a yi wa gaɓar ruwan ɗumin har sai bayan kwana uku.
4) Kada a shafa mai ko wani magani mai zafi a targaɗen.
Source: Physio Hausa
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/