Ya bayyana hakane a yayin da yake magana da sojojin dake yaki da Boko
Haram din a Borno inda yace kamin karshen shekararnan ko kuma zuwa
karshenta zasu gama da Boko Haram.Yace dan haka sojojin su mayar da hankali wajan cimma wannan Buri.
Yace shugaba Buhari ya basu taimako da goyon baya wanda su taba samu ba a baya.Yace
hakanan hukumar sojojin zata ci gaba da baiwa sojojin duk kwarin gwiwar
da ya kamata. Yace ya gamsu sosai da yanda sojojin suke aiki.Abubakar
yace sun samu jiragen yaki 22 sannan kuma akwai 16 dake kan hanya.
Yace wadannan jirage sun taimaka matuka wajan nasarorin da suke samu inda yace idan suka ci gaba da haka nan bada jimawa ba zasu zama sojojin sama mafiya karfi a Africa.
Hutudole
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari