Mun yafe wa matar dan uwan mu da ta yanke masa azzakari>>>Inji dan uwansa

Ranar Talata, 30 ga Yuni, 2020, wata rana ce da Aliyu Umaru, ba zai taba mantawa ba a rayuwarsa saboda a wannan rana uwargidarsa, Halima, ta guntule masa azzakari da wuka. Yana kwance yanzu a asibiti cikin radadin jiki da zuciya a asibitin koyarwan gwamnatin tarayya dake Gombe, inda aka kaisa bayan aukuwan hadarin.

A asibitin, an ga yadda Likitoci suka sanya masa na'ura na musamman domin taimaka masa wajen fitsari yayinda aka ajiye azzakarinsa da matar ta yanke gefe guda cikin leda. A hirar da jaridar Punch tayi da shi, Aliyu Umar ya bayyana irin iftila'in ya shiga ciki.

Yace: "Ni dillalin Likitocin dabbobi ne. Ina sayar da magungunan dabbobi. shekaru na 42 kuma ina da mata biyu da yara biyu." "Ni mazaunin garin Tella ne a karamar hukumar Gassol a jihar Taraba. An turo ni asibitin koyarwan tarayya Gombe ne daga FMC Taraba." "Bayan dawowa na daga aiki, na debi ruwa don yin wanka kuma na ci abincin da iyalina ta girka kuma nayi bacci. Daga baya wani mugun azaba ya tasheni daga barci ina iwu." "Uwargidata ta yanke min 'bura'.

A lokaci aka sanar da makwabta. Ban sani ba (akwai yiwuwan) an sanya magani cikin abincin saboda yadda nayi bacci mai zurfi. Matata ta lalata min rayuwa kuma akwai takaici." Rahotanni sun nuna cewa Halima ta kasance cikin takun tsaka da mijinta da kishiyarta. Dan'uwan Umaru, Malam Usman ya bayyana cewa yana gidansa cikin dare aka kirashi a waya cewa akwai matsala.

Yace: "Cikin dare wayata ta fara kara, ashe yayana. Ya fada min abinda ya faru da shi. Da wuri aka garzaya da shi FMC Taraba domin tsayar da jinin dake kwarara da kuma yi masa tiyata." "Amma suka kasa yin aikin saboda sun ce basu da isasshen kayan aiki.

Sai suka bamu shawaran kai shi wani asibitin daban." "Ita kuma mun fadawa mutane kada wanda ya taba ta. Aikin gama ya gama kuma babu yadda zamuyi. Mun barta da Allah. Babu abinda zamuyi mata da zai dawo da azzakarin 'danuwana."

Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari



Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN