Na kama matata a ƙarƙashin gadon kwartonta tsirara - Miji ya faɗa wa kotu


Wani mutum mai suna Olalekan ya bukaci kotun gargajiya da ke Ojo Oba/Mapo ta raba aurensa da matarsa, Anudetan domin ya dena ƙaunar ta. A cewar magidanci yana son a raba auren su ne saboda halin rashin sanin ya kamata da rashin kulawa da ta ke da shi.

Ya ƙara da cewa tana bin maza kuma ta gudu ta bar shi ƴarsu na tsawon shekara hudu kamar yadda The Nation ta ruwaito. Olalekan ya kuma roki kotun ta bashi daman rike ƴarsu mai shekara biyar da watanni shida. Anudetan ta amince da bukatar raba auren da mijinta ya gabatar wa kotu inda ta ce ba ta taɓa samun natsuwa ba a auren.

Yadda na kama matata ƙarƙashin gadon kwartonta tsirara - Miji ya faɗa wa kotu. Hoto daga The Cable Source: UGC Ta kuma amince a bar wa tsohon mijinta ƴarsu amma a bata damar ganinta duk lokacin da ta buƙata.

Shugaban Kotun, Cif Ademola Odunade bayan sauraron bangarorin biyu ya yanke hukuncin raba auren inda yace bisa dukkan alamu bangarorin biyu ba su son auren. Odunade ya haramtawa wacce aka yi kara zuwa gidan wanda ya yi karar inda ya ce duk lokacin da ta ke son ganin ɗiyarta sai su haɗu a kotu. Tunda farko, Olalekan ya shaidawa kotu cewa, "roƙon da na ke yi wa wannan kotun shine ta raba aure na da matata a yau.

"Anudetan ta cika bin maza kuma za ta kashe ni idan na cigaba da zama da ita. "Matata tana shayar da ɗiyar mu (lokacin tana wata shida) amma ta fara lalata da wani mutum da ke kusa da gidan mu. "Matar da ke da gidan ta sanar da ni abinda ke faruwa ta ce matata ta saba zuwa gidan. "Ta shaida min cewa ta yi wa matata gargadi amma ba ta dena ba.

Hakan yasa ta karbi lambar waya ta tace za ta kira ni duk lokacin da matata ta zo gidan. "Kwana ɗaya bayan karɓar lambar sai naji kiran ta sai ni da ƴan uwa na muka taho a babur. "Ta nuna mana ɗakin mutumin muke Kwankwasa ya bude muke leƙa amma ba mu ga kowa ba sai shi kaɗai. "Har zamu tafi amma ta ce mu sake duba wa sai na koma na bincika ƙasar gado sai ga Anudetan tsirara a ƙarƙashin gado.

"A fusace na fito da ita har zan duke ta amma na daure sai dai na mata gargadin kar ta dawo gida na, na tafi na kwaso kayan ta na kai gidan saurayin nata."A bangarenta, wacce aka yi kara ta ce mutumin da aka gano ta a gidansa ba saurayinta bane, ta ce saurayin kawar ta ne kuma sun tafi wurinsa neman kudi ne amma kawar ta dan fita tayi wani hidima ta dawo.Kwatsam kuma sai ka mijinta da dan uwansa sun shigo gidan sune neman cin mutuncin mutumim.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari



Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN