Wata yarinya mai shekara 14 a kasar Afghanistan ta sha yabo a shafukan intanet bayan ta harbe yan ta'addan Taliban guda biyu bayan sun kashe iyayenta.
Yan Taliban sun farmaki kauyen Ghor suna neman basaraken kauyen wanda ke goyon bayan gwamnati. Bayan sun same shi sai suka jawo shi tare da matarsa suka harbe su har lahira a haraban gidansa a gaban idon diyarsa Gul.
Bayan ganin yadda aka kashe iyayenta, diyar basaraken Qamar Gul, ta shiga daki ta dauko bindiga kirar AK47 na mahaifinta ta harbe yan Taliban biyu da suka kahe mahaifanta har lahira ta jikata da dama saura kuma suka ruga da gudu suka shige daji.
Shugaban yan sandan yankin Habiburahman Malekzada, ya ce Gul ta kashe yan Taliban biyu da suka kashe iyayenta. Bayan sauran yan Taliban sun tsere, daga bisani sun dawo suka farmaki kauyen Ghor, amma kauyawan suka turje harin kuma suka mayar da martani da harbe harben bindigogi.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/