Ko akwai alaka cin jan nama da ciwon guiwa? duba wannan bayani

Miliyoyin mutane a faɗin duniya ne ke fama da ciwon gaɓɓai sakamakon larurori daban-daban. Matsalar ciwon gaɓɓai na da illar gaske ga ingancin rayuwa, tattalin arziƙi da walwala.

A wani lokacin ma idan matsalar ta ta'azzara na iya nakasa mutum, sannan ta tsugunar da shi ɗungurugum.

Sai dai wani abun mamaki shi ne yadda mutane ke alaƙanta ciwon gaɓɓai musamman ciwon gwiwa da yawan cin jan nama. Wannan ya sa da zarar mutum ya fara ƙorafin ciwon gwiwa sai ka ji an ce masa "ka rage cin jan nama".

To ko yaya lamarin yake?

Da farko dai ya kamata mu fahimci cewa ciwon gwiwa iri-iri ne kuma kowanne na da sababinsa. Saboda haka, ba abu guda ne ke kawo duk ire-iren ciwon gwiwa ba.

Ire-iren cutukan gaɓɓai da ka iya janyo ciwon gwiwa sun haɗa da:

1) Amosanin gaɓa: Amosanin gaɓa wato 'osteoarthritis' a turance, ciwon gaɓa ne sakamakon zaizayewar gurunguntsin gaɓa yau da gobe, musamman a gaɓɓai maɗauka nauyin jiki kamar gwiwar ƙafa.
2) Sanyin ƙashin gaɓa, wato 'rheumatoid arthritis' a turance. Sai dai sanyin ƙashin gaɓa ya fi shafar ƙananun gaɓɓai kamar gaɓɓan yatsun hannu da ƙafa.
3) Ciwon gaɓa na shigar ƙwayar cuta gaɓa ko jiki, wato 'septic arthritis' a turance. Irin wannan ciwo na iya kama kowacce gaɓa idan ƙwayar cuta kamar bakteriya ta kama jiki gaba ɗaya ko kuma wata gaɓa guda.
4) Ciwon gawut, wato 'gout arthritis' a turance, ciwon gaɓa ne da ke faruwa sakamakon taruwar gishirin "urate" a cikin gaɓa.
5. Ciwon gaɓa na bugu/rauni: Irin wannan ciwon gaɓa na faruwa musamman ga masu wasannin tsalle-tsalle da guje-guje kamar 'yan ƙwallon ƙafa da dai sauransu.

Misali, sakamakon lahani ga gurunguntsin gaɓa ko gammon gwiwa (meniscal tear). Ko kuma yayin da haɗarin abun hawa ya ritsa da mutum kuma ya samu karaya a kan gaɓa, wannan na iya lalata muhimman sassan kariya da ke cikin gaɓar ya haifar da ciwon gwiwa.

To ko wanne irin ciwon gwiwa ne ke da alaƙa da cin jan nama?

Daga cikin ire-iren cutukan gaɓa da ke janyo ciwon gaɓa wanda ake alaƙantawa da yawan cin jan nama shi ne ciwon gawut, wato "gout athritis" kamar yadda muka ambata a sama.
Yadda ciwon gawut ke faruwa

A al'adance, jikin mutum na samar da sinadarin 'purines', yayin da jiki ya narka wannan sinadari zai haifar da wani sinadari da ake cewa 'uric acid'. Sinadarin 'uric acid' zai narke ya bi jini sannan ƙoda ta tace shi zuwa cikin fitsari.

Amma duk lokacin da jiki ya samar da sinadarin 'purines' da yawa saboda yawan cin nau'in abinci/abinsha da ke ɗauke da sinadarin 'purines' ko kuma yayin da ƙoda ta gaza tace sinadarin 'uric acid' zuwa cikin fitsari, wannan zai haifar da taruwar sinadarin 'uric acid' a cikin jini fiye da ƙima.

Haka nan, taruwar sinadarin 'uric acid' a cikin jini fiye da ƙima zai sa ya riƙa duddunƙulewa har ya zama gishirin "urate". Wannan gishiri na 'urate' shi ne ke taruwa a cikin gaɓɓai ya haifar da ciwon gawut wanda ke haddasa matsanancin ciwo, kumburi da riƙewar gaɓɓai.

Bugu da ƙari, akwai nau'o'in abinci/abinsha daban-daban da muke ci yau da gobe waɗanda ke danƙare da sinadarin 'purines' a ciki. Kuma cin irin waɗannan abinci/abinsha fiye da ƙima na iya kawo hauhawar sinadarin 'uric acid' a cikin jini wanda kuma daga ƙarshe zai haifar da ciwon gawut.

Daga cikin abinci/abinsha da ke ɗauke da sinadarin 'purines' akwai:

1. Jan nama, kamar naman saniya, rago
2. Naman kayan ciki, kamar hanta, ƙoda, matsarmama
3. Naman ruwa, kamar jatan lande (shrimp), kifi sadin (sardines), 'lobster', 'mussels', 'anchovies'
4. Barasa/giya, abinci/abinsha da ke ɗauke da siga nau'in 'fructose' kamar lemukan roba, askirim (ice cream), alawar cakulet da sauransu.

Har wa yau, ganyayyaki kamar alayyahu (spinach) da shekan ɓera (asparagus) na ɗauke da sinadarin 'purines' sosai, sai dai bincike ya tabbatar da cewa sinadarin 'purines' da ke cikin alayyahu da shekan ɓera ba ya janyo hauhawar sinadarin 'uric acid' a cikin jini. Saboda haka basu shiga jerin abubuwan da mai ciwon gawut zai ƙaurace wa ba.

Yaushe za a fara ƙaurace wa waɗannan abinci/abinsha da aka lissafa?

Za a fara bayar da tazara ko ƙaurace wa cin irin waɗannan nau'o'in abinci/abinsha ne da zarar likita ya tabbatar cewa mutum na fama ciwon gawut.

Amma mutum zai iya ci gaba da cin waɗannan nau'o'in abinci/abinsha matuƙar ba a tabbatar yana da ciwon gawut ba ko kuma babu ƙorafin ciwo ko kumburin gaɓɓai a jikinsa. Sai dai, a har kullum mafi kyawun al'amari shi ne tsaka-tsakinsa.

Ta yaya za a gane ciwon gwiwa daga ciwon gawut ne?

Ana gane ciwon gwiwa na da alaƙa da ciwon gawut idan aka samu alamun ciwo, kumburi, rirriƙewar gaɓɓai a sauran gaɓɓan jiki musamman gaɓar babban yatsan ƙafa.

Bayan duba waɗannan alamu, likita zai nemi a gwada jinin mutum don duba ƙimar sinadarin 'uric acid' a cikin jini. Za a gane ciwon gawut ne idan sakamakon gwajin ya nuna sinadarin 'uric acid' ya hau fiye da ƙima a cikin jini.

Daga nan kuma sai likita ya bayar da magungunan da za su temaka wajen daidaita sinadarin 'uric acid' a cikin jini.

Sannan a gayyaci likitan fisiyo (physiotherapist) don ci gaba da lura da matsalolin ciwon gaɓɓai, kumburi da rirriƙewar gaɓɓai. Likitan fisiyo zai yi duk mai yiwuwa wajen magance waɗannan matsaloli don mutum ya ci gaba da rayuwarsa cikin karsashi da walwala. Domin shan maganin kawai ba tare da ganin likitan fisiyo ba na da haɗarin kassarewar aikin gaɓɓai, wato nakasa.
Alamomin ciwon gawut

Daga cikin alamomin sun haɗa da:

1. Matsanancin ciwon gaɓɓai; ciwon na iya kama kowacce gaɓa saɓanin zaton cewa iya gwiwar ƙafa ciwon gawut ke kamawa kawai.
2. Kumburin gaɓɓai, jin ciwo idan aka taɓa/matsa gaɓar da ta kamu, sannan bayan gaɓɓan sun kumbura, za su yi ja kuma.
3. Rirriƙewar gaɓɓai yayin hutu da kuma yayin ayyukan yau da kullum.
4. Idan ciwon gawut ya ta'azzara, a kan ga bayyanar bulli, wato kamar taruwar ruwa a ƙarƙashin fata a gefen gaɓɓan, kamar gaɓɓan gwiwar hannu, idan sawu da sauran sassa.
Abubuwan da ke da ƙara haɗarin kamuwa da ciwon gawut sun haɗa da:
1. Abinci/abinsha da ke danƙare da sinadarin 'purines' [duba jerinsu a sama].
2. Ƙiba/teɓa: Jikin mai ƙiba na samar ya sinadarin ''uric acid' da yawa kuma ƙoda kan sha wahalar tace sinadarin zuwa cikin fitsari.
3. Sanannun cutukan jiki: Ga duk wanda ya san yana fama da wasu cutuka kamar hawan jinin da ba a shawo kansa ba, ciwon siga, ciwon ƙoda da sauransu na da haɗarin kamuwa daga ciwon gawut.
4. Jinsi: Maza sun fi kamuwa da ciwon gawut fiye da mata. Maza kan kamu da ciwon gawut tsakanin shekara 30 zuwa 50, yayin da mata kuma kan sami jinkirin samun alamun ciwon gawut har sai bayan sun daina haila.
5. Samun ciwon gawut a dangi: Samun mai ciwon gawut a cikin dangi na nuni da cewa wani a dangin na da haɗarin samun ciwon.

Daga ƙarshe, ina fatan mun gane ire-iren ciwon gaɓa da sabubansu, sannan mun gane alaƙar cin jan nama da ciwon gwiwa, kuma mun gane cewa ba kowanne irin ciwon gwiwa ne ke da alaƙa da ciwon gwiwa ba.

Duba da haka, da zarar ka fara fuskantar alamun da muka ambata, tuntuɓi likitan fisiyo a asibiti mafi kusa da kai don duba ka.

Source: Physio Hausa

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN