'Yan bindiga sun sace yar wata biyar tare da mata 17 a Katsina

Al'ummar garin Zakka a jihar Katsina sun ce wasu 'yan bindiga da ba su san ko su waye ba sun kai masu hari inda suka sace mata 17 da kuma kwashe shanu da dukiyoyinsu.

Wani mazauni garin na Zakka da ke cikin ƙaramar hukumar Safana ya shaida wa BBC cewa ƴan bindigar sun shiga garin ne tsakar daren Lahadi inda suka shafe sama da sa'a biyu suna fashi.

Ya ce Æ´an bindigar sun shigo garin ne misalin karfe 12 na dare kuma suka fara harbin bindiga wanda ya razana mutanen garin wasu suka ruga daji wasu kuma suka boye a cikin karan dawa da gero.

"Sun kwashe shanu da dama da tumaki sannan suka shiga gida gida suna kwatar dukiyar mutane kafin su tafi da mata da 'yan mata 17," inji shi.

Amma ya ce É“arayin sun mayar da wata yarinya Æ´ar wata biyar da haihuwa da kuma hudu daga cikin matan da suka É—auka da ya ce suma Allah ya kuÉ“utar da su. 

Ƴan bindigar dai ba su kashe kowa ba a garin na Zakka wanda a bara aka taba kai wa hari.
Babu dai wani bayani da ya fito daga jami'an tsaro game da harin.

Jihar Katsina na É—aya daga cikin jihohin da 'yan bindiga ke ci gaba da cin karensu babu babbaka a yankin arewa maso yammacin Najeriya.

Rahotanni daga wasu ƙauyuka na jihar irin su Batsari da Dutsinma da Jibiya da Faskari na cewa kaso mai yawa na manoman yankin ba su yi sharar gona ba a wannan shekara ballantana niyyar fara noma sakamakon matsi da suke fuskanta daga 'yan bindiga.

Source: BBC
 

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN