• Labaran yau


  Yanzu-yanzu: DSS ta cafke Ibrahim Magu shugaban hukumar EFCC

  Hukumar 'yan sandan fararen kaya (DSS) ta kama Ibrahim Magu, mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa tare da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC).

  An damkesa ne bayan kwanaki kadan da Abubakar Malami, antoni janar kuma ministan shari'ar Najeriya ya zargesa da almundahana. Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, shugaban EFCC ya yi tafiya zuwa birnin Dubai da ke daular larabawa ba tare da sanin shugaban kasa Muhammadu Buhari ba kuma a yayin kullen kasa.

  A lokacin da aka tuhumesa, ya ce ya je wani bincike ne. Ana zargin shugaban da rayuwar da ta fi abinda yake samu daga aikinsa.

  Legit


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yanzu-yanzu: DSS ta cafke Ibrahim Magu shugaban hukumar EFCC Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama