Cikakken rahotun abin da ya faru da Ibarahim Magu shugaban EFCC bayan an tare shi a Wuse 2 Abuja

Legit Hausa

'Babu hannunmu': DSS ta yi karin haske a kan kama Ibrahim Magu


Hukumar jami'an tsaro na farin kaya (DSS) ta ce ba ta kama mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, ba.

A cikin wata sanarwa da jami'an hulda da jama'a, Peter Afunanya, DSS ta ce babu gaskiya a cikin labarin da wasu kafafen yada labarai ke yadawa a kan cewa ta kama Magu.

"Hukumar DSS ta na son sanar da jama'a cewa ba ta kama Ibrahim Magu, mukaddashin shugaban hukumar EFFC, ba kamar yadda wasu kafafen yada labarai suka bayyana ba.

"DSS ta fitar da wannan sanarwa ne a yau, Litinin, 6 ga watan Yuli, bayan yawan tuntubarta a kan zargin kama Magu," a cewar sanarwar. Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

An gayyaci Ibrahim Magu, shugaban EFCC amsa tambayoyi


An gayyaci mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, (EFCC) gaban kwamiti don bayani a kan ayyukan hukumar.

An gano cewa, kwamitin na wannan zaman ne a 'Banquet Hall' da ke fadar shugaban kasa. An tsare Magu a cunkoson motoci da ke wucewa zuwa anguwar Wuse II na EFCC a Abuja kuma aka mika masa goron wannan gayyatar.

Duk da Magu na kan hanyarsa ta zuwa hedkwata, ya roki jami'in da ya tsaresa a kan ya bar sa inda daga baya sai ya amsa wannan gayyatar. Amma kuma an sanar da shi cewa gayyatar wannan kwamitin ta fi muhimmanci. Wurin karfe 1:35 na rana, Ibrahim Magu ya isa fadar shugaban kasa inda aka shigar da shi inda zai yi bayanan.

A wannan lokacin, lauyan Magu, Rotimi Oyedepo, ya samesa a fadar shugaban kasar. Wata majiya ta ce: "Magu da Jacob a halin yanzu suna wani ofishin da ke fadar shugaban kasar. "Ba a kama shi ba, kuma babu wata hukumar tsaro da ta damke shi. Muna sauraron ci gaban da zai faru a gaba.

DSS ta hana 'yan jarida shiga inda ake tuhumar Magu a Aso Villa


A ranar Litinin, jami'an hukumar tsaro na farin kaya, sun hana manema labarai shiga dakin taron da shugaban hukumar yaki da rashawa (EFCC), Ibrahim Magu ke amsa tambayoyi.

A ranar Litinin ne labarin damke Magu ya fara yaduwa wanda ake zargin hukumar tsaro ta farin kaya tayi. Amma kuma, manema labaran gidan gwamnati sun gangara dakin taron da shugaban EFCC yake don tabbatar da wannan ci gaban.

Sai dai kuma jami'an DSS wadanda ke dankare a farfajiyar domin taron sun umarci manema labarai da su bar wurin, jaridar The Nation ta ruwaito. "Sun ce ku hakura da amfani da wannan wurin na yau," wani jami'in ya sanar da manema labarai cike da tausasa murya.

Da farko dai Legit.ng ta rahoto cewa an gayyaci mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, (EFCC) gaban kwamiti don bayani a kan ayyukan hukumar. An gano cewa, kwamitin na wannan zaman ne a 'Banquet Hall' da ke fadar shugaban kasa.

An tsare Magu a cunkoson motoci da ke wucewa zuwa anguwar Wuse II na EFCC a Abuja kuma aka mika masa goron wannan gayyatar. Duk da Magu na kan hanyarsa ta zuwa hedkwata, ya roki jami'in da ya tsaresa a kan ya bar sa inda daga baya sai ya amsa wannan gayyatar.

Amma kuma an sanar da shi cewa gayyatar wannan kwamitin ta fi muhimmanci. Wurin karfe 1:35 na rana, Ibrahim Magu ya isa fadar shugaban kasa inda aka shigar da shi inda zai yi bayanan. A wannan lokacin, lauyan Magu, Rotimi Oyedepo, ya samesa a fadar shugaban kasar.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari



Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN