• Labaran yau


  Yansanda sun kama Namalika wanda ake zargin ya kashe Likita a Zamfara ya kone gawarsa

  Yansandan jihar Zamfara sun kama wani mai suna Abubakar Namalika bisa zargin kashe wani Likita mai suna Dr. Enoch Okpara a Gusau.

  Ranar 13 ga watan Yuni ne aka tarar an kashe tare da kona gawar wannan Likita a gidansa da ke unguwar Mareri a birnin Gusau.

  Kwamishinan yansandan jihar Zamfara Usman Nagogo ya shaida wa manema labarai haka.

  Ya ce yansanda sun kama Namalika ne yayin da suke kokarin aikata wani laifin, amma sauran yan gungun nashi sun gudu.

  Ya ce Namalika ya shaida wa yansanda cewa su ne suka aikata laifin, sun je gidan Likitan ne domin su karbi kudi ko ta halin dole, bayan basu sami kudi a wajensa ba sai suka kashe shi suka kone gawarsa.  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yansanda sun kama Namalika wanda ake zargin ya kashe Likita a Zamfara ya kone gawarsa Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama