Legit
A ranar Litinin, misalin karfe 5:30 na yamma dakarun sojin 198 Special Forces Battalion sun gamu da iftila'in bama-baman da aka shuka cikin kasa yayin sintiri a Mainok, hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.
Humangle ta ruwaito cewa Bam din ya tashi da Sojin inda yayi sanadiyar mutuwar Hafsan Soja daya, Abdullahi Alhassan, mai matsayin 2nd Laftanar yayinda wasu Soji biyu suka jikkata.
Dakarun Sojin fiye da 12 na cikin motocin yaki biyu ne lokacin da Bam din ya tashi.
Irin haka ya faru a makon da ya gabata inda rundunar sojin Operation Lafiya Dole sukayi arangama da shukakken Bam.
Hafsa daya mai matsayin Lafatanal ya rasa ransa yayinda wani abokin aikinsa yayi mumunar jikkata.
Bama-baman da yan ta'addan ke shukawa da hare-haren kwantan bauna sun cigaba da zama manyan kalubale ga Sojojin Najeriya dake yakan yan ta'addan Boko Haram da ISWAP a Arewa maso gabas.
Hakazalika Sojojin basu da isassun kayayyakin kariya daga ire-iren bama-baman nan.
A watan Junairu, yan ta'adda sun kaiwa Sojojin Najeriya farmaki a wajen kauyen Mainok, hakazalika a Mayu, sun kara kaiwa Sojin 156 Battalion dake Mainok mumunan hari.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari