Matashin mai suna Abdussalam Ibarahim wanda dalubine dake matakin aji na 2 a jami’ar jihar Bauchi.
An rawaito cewa Mahaifiyar matashin Aisha Ibrahim, ta kai rahoto ga kungiyar ‘yan vigilante don yiwa dan nata horo, saboda zarginsa da take na satar mata turmin zani.
Wani makoci na kusa, mai suna Ningi, ya shaida ce wa, Aisha ta zargi danta da satar turmin zani Wanda aka kiyasta bai kai N3,000 ba.
Ya kara da cewa bayan da ta tuhume shi kuma Abdulsalam ya musanta wannan zargi, Aish ta gayyaci kungiyar ‘yan sakai wanda takai da sun jikkata shi har yayi sanadin mutuwarsa.
Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda na jihar, Ahmed Wakil, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce hakika wannan laifin kisan kaine suka aikata.
Ya kuma tabbatar da kame mutane uku da ake zargi da hannu a lamarin.
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari