Shekara 93: Kai Dattijon amana ne wanda bai da kabilanci - Dalung ya gaya wa Sheikh Dahiru Bauchi

Tsohon Ministan wasanni na Najeriya karkashin mulkin shugaba Muhammadu Buhari, watau Solomon Dalung, ya taya Mashahurin Malamin addinin Musulunci Sheikh Dahiru Bauchi cika shekara 93 a doron Duniya.

Dalung ya sanar a shafinsa na sada zumunta cewa " Shehu dan Najeriya ne da baya da kabilanci kuma wanda ke mutunta fahimtar jama'a. Dagewarsa na ganin an sami zaman lafiya tsakanin manyan addinai biyu na Najeriya ya sa ya zama abin koyi kuma jagora na amana".

" Ina kaunarka da gaske Malam, kuma ina fatan Allah ya kara jan zamaninka cikin albarka, barka da cika shekara 93.".

Wadannan su ne wasu daga cikin kalaman Solomo Dalung ga Sheikh Dahiru Bauchi.

A kula: An dauki wannan hoto ne a 2017.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabariPrevious Post Next Post