Uba ya dirkawa dansa harsashi wajan gwajin maganin Bindiga dan kariya daga harin Fulani

Wani uba a ya karbo maganin Bindiga dan baiwa danshi kariya daga Harin Fulani makiyaya, an yi rahin saa maganin bai yi ba inda ya durkawa dan nasa harsashi.Saidai abin farin ciki shine dan nasa bai mutu ba,

Ya tsira. Daniel Qudus dake bayyana yana yanda lamatin ya faru a hannun ‘yansandan jihar Oyo ya bayyana cewa dansa yana dawowa gida daga gona da dare kuma akwai matsalar Fulani Makiyaya dake kai musu hari, yace wannan ne yasa dole ya dukufa nemarwa dansa maganin bindiga.

Ya kara da cewa ya je wajan wani me bada maganin gargajiya inda ya samo maganin kuma yace masa idan yazo gida ya gwada. Yace wajan gwajine sai aka harbi danshi.Shima dai wanda ya bayar da maganin,

Akiyemi ya bayyana cewa shi ba maganin bindiga ya baiwa Daniel ba, maganin habakar kasuwanci ya bashi. Yace kawai yana zaune sai ga Daniel da danshi jinajina wai ya cire masa harsashin dake jikinshi. Yace ko kulashi bai yi ba tunda shi ba likita bane.

Kwamishinan ‘yansandan jihar, Mr. Nwachukwu Enwonwu ya bayyana cewa duka wanda ake zargin za’a gurfanar dasu gaban kuliya.

Hutudole


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabariPost a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN