Ko akwai cikakkiyar matsaya game da ƙayyade adadin ƙwai da mutum zai ci a sati?

Ƙwan kaji na daga cikin nau'in abinci mai inganci na yau da kullum, saboda araharsa da kuma sauƙin sarrafawa. Babban ƙwai guda na da nauyin giram hamsin (50 g) ne, kuma a maƙare yake da furotin (6 g), kwalastaral (200 mg), daskararren mai (1.56 g), tsinkakken mai (2.76 g), nau'o'in bitamins, ɓirɓishin ma'adanai, da sauran muhimman sinadarai masu matuƙatar amfani ga lafiyar jiki.

[Furotin, wato 'protein' kenan a turance, ajin abinci ne mai gina jiki. Kwalastaral kuwa, nau'in mai ne da ke cikin ajin kitse / mai a cikin ajujuwan abinci. Kuma bitamins na nufin 'vitamins' a nan.]

Yawancin mutane sun fi son cin ƙwanduwar ƙwai fiye da farin ƙwan, saboda ta fi daɗi a cewarsu, musamman ga waɗanda ke zaton cewa ƙwanduwar ce ke ɗauke da furotin a cikin ƙwan. Sai dai wannan zato saɓanin abin da bincike ya tabbatar ne. Saboda, farin ƙwan shi ne ke maƙare da furotin. A yayin da ƙwanduwar kuma ke ɗauke da kwalastaral da kuma daskararren mai, waɗanda tsawon shekaru akai ta kai ruwa rana kan tabbaci ko akasin illarsu ga lafiya musamman wajen haddasa ciwo zuciya.

[Daskararren mai, wato 'saturated fat' a turance, nau'in mai ne da ke cikin ajin kitse / mai. Kuma shi ne irin man da ke daskarewa ko yai bacci haka kawai, misali, kakide/kitse, man shanu, manja da sauransu.]

Saboda yawan kwalastaral da ƙwai ke ɗauke da shi, hakan ya sa tsawon lokaci mutane ke ci gaba da ƙaurace wa cin ƙwai akai-akai, a ƙoƙarin rage yawan kwalastaral daga cimaka. Musamman, bayan da hukumomin kiwon lafiya suka zargi kwalastaral daga cimaka da haddasa ciwon zuciya sun ƙayyade cinsa zuwa miligiram ɗari uku (300 mg) a kullum, kafin daga bisani hukumomin su yi watsi da ƙayyade ƙwalastaral ɗin a shekara ta 2015. Watsi da ƙayyade yawan ƙwalastaral ɗin da mutum ya kamata ya ci a rana ya biyo bayan sabbin bincike da suka nuna rashin haɗarin ƙwalastaral daga cimaka ga zuciya kamar ƙwai.

Kwalastaral muhimmin tubali ne wajen ginin bangon ƙwayar halitta, wato 'cell menbrane' a turance, baya ga kasancewarsa muhimmi wajen sarrafa wasu sinadaran jiki.

Haka nan, hanta ce ke samar da mafi yawan kwalastaral da jiki ke buƙata. Amma a yayin da kwalastaral daga cimaka ya ƙaru, hanta za ta rage yawan wanda take samarwa domin samun daidaiton kwalastaral a cikin jini.

Bugu da ƙari, kwalastaral ya kasu gida biyu: akwai mai ƙyau, akwai mara kyau. Kwalastaral mai kyau shi ne yake yashe ko wanke kwalastaral mara kyau daga cikin jini. Domin kwalastaral mara kyau shi ne ke kwanciya kuma ya toshe jijiyoyin jini kaɗan da kaɗan, musamman a zuciya har ya haifar da bugun zuciya.

Bincike daban-daban da aka gudanar sun nuna cewa babban abin da ke kawo hauhawar kwalastaral mara kyau a cikin jini shi ne daskararren mai, saɓanin kwalastaral da ke cikin ƙwai. Saboda haka, babu buƙatar ƙaurace wa cin ƙwai don rage ko ƙayyade kwalastaral.

Kuma cin ƙwai ɗaya ko biyu kullum ba shi da haɗarin haddasa ciwon zuciya, saboda daskararren man da ke cikin ƙwai (1.56 g) ƙalilan ne idan aka kwatanta shi da sauran nau'o'in abinci da suke danƙare da daskararren mai kamar naman shanu, madarar shanu, man shanu, cukwi, fatar kaji, askirim, da sauransu.

Haka nan, man tsirrai kamar man kwakwa, manja da man kwakwar manja na ɗauke da daskararren mai sosai. Har wa yau, man gyaɗa ma na ɗauke da daskararren mai, sai dai yawansa bai kai na waɗanda muka ambata a sama ba.

Daga ƙarshe, babu damuwa ko ɗar-ɗar ga duk mai son sanya ƙwai cikin ƙunshin abincinsa na yau da kullum duba da alfanunsa. Saboda i zuwa yanzu, babu cikakkiyar matsaya game da ƙayyade adadin ƙwan da mutum zai ci zuwa wani adadi, saɓanin tsohuwar matsayar da ta ƙayyade cin ƙwai zuwa uku ko huɗu a sati.

Sai dai, duk da janye matsayar ƙayyade cin ƙwai da hukumomin kiwon lafiyar suka yi bayan kuɓutar kwalastaral da ƙwai ya ƙunsa daga zargin haddasa ciwon zuciya, akwai buƙatar rage cin nau'o'in abincin da ke danƙare da daskararren mai wanda yake ingiza hauhawar kwalastaral mara kyau da ke da haɗarin janyo ciwon zuciya.

Physio Hausa
 

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN