• Labaran yau


  Yadda ya kamata ka riƙe wayar salula don guje wa ciwon wuya.

  Matsakaicin kan mutum yana kaiwa nauyin kilogiram huɗu (4 Kg). Amma nauyin kan yana riɓanya har sau biyu yayin da mutum ya sunkuyar da kansa kimanin kowanne digiri goma sha biyar (15 degrees).

  Abin nufi a nan shi ne; riɓanyar nauyin shi ne riɓanyar aiki ko wahalar da tantanai da tsokokin wuya ke sha wajen riƙe kan. Haka nan, ƙarin wannan aiki ko wahala na jefa tsokokin shiga ɗabi'un da za su haifar da ciwon wuya.

  Yayin amfani da wayar salula, kwamfuta ko na'urar wasan yara, tabbatar kanka a miƙe yake ba tare da sunkuyawa ba. Wannan zai rage haɗarin samun ciwon wuya.


  Domin haka, kasance ka ɗaga na'urar sama daidai da idonka maimakon sunkuyar da kai.
   
  #Ergonomics
  #Pathognomics
  #Pathokinesiology

  Source: Phusio Hausa
   

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yadda ya kamata ka riƙe wayar salula don guje wa ciwon wuya. Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama