• Labaran yau


  Uwa ta amince wa makwabci amma ya yi wa daiyarta mai shekara 2 fyade a Adamawa

  Jami'an yan sandan jihar Adamawa sun cafke wani saurayi mai shekara 18 bisa zargin yi wa diyar makwabcinsa mai shekara 2 fyade a Jimeta ranar Talata 28 ga watan Yuli.

  Kakakin yan sandan jihar Adamawa DSP Sulaiman Nguroje ya shaida wa manema labarai cewa wanda ake zargin yana da shago kusa da na uwar yarinyar wanda makwabciyarsa ce wanda aka amince da shi, amma sai ya kai yarinyar wata Makarantar firamare na Bekaji inda ya aikata mata fyade.

  Nguroje ya ce " Mahaifiyar yarinyar ta kula  cewa al'aurar yarinyar ya kumbura, daga bisani kuma ta shigar da kara a wajen yansanda".

  Ya ce yanzu haka an kama wanda ake zargi kuma yana amsa tambayoyi saboda ana ci gaba da bincike, yayin da aka kai yarinyar wani asibiti domin samun kulawa daga Likitoci.


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Uwa ta amince wa makwabci amma ya yi wa daiyarta mai shekara 2 fyade a Adamawa Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama