Wanda aka kama mai suna Muhammad Sani Umar (Tela) ana zargin ya yi wa yarinyar fyade har sau biyu kuma ya bata N80.
Sahara Reporters ta ruwaito cewa asiri ya tonu nebayan yarinyar ta kamu da rahin lafiya, bayan wani lokaci mahaifiyarta ta kula cewa wani abu yana faruwa da yarinyar, sakamakon haka ta tambayeta ita kuma yarinyar ta kai mahaifiyar wajen wannan tsoho kuma daga isar su shagonsa sai yarinyar ta nuna shi da hannunta.
Ganin yarinyar da mahaifiyarta ke da wuya, tsoho bai yi gardama ba sai ya fara bayar da hakuri yana cewa a rufa masa asiri zai dauki nauyin jinyar yarinyar.
Nan take mahaifiyar yarinyar ta fasa kuwa jama'a suka taru kuma aka yi wa tsoho dan karen duka kuma aka kai shi gidansu yarinya inda ya yi bayani, kuma aka kara lafta masa na jaki daga matasa majiya karfi.
Daga bisani an mika shi ga jami'an yansanda domin fuskantar tuhuma a gaban Kotu.
Mahaifiyar yarinyar ta roki mahukunta cewa a yi ma diyarta adalci a kan lamarin, domin wannan tsoho yana da daurin gindi a wajen manya a Chanchaga da jihar Niger.
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari