Duba dalili da ya sa wata mata 'yar sanda ta harbi mijinta da bindiga AK47 har sau biyu ta gudu

Jami'an yansanda a kasar Kenya suna neman wata mata yar sanda bayan ta harbi mijinta da bindiga kirar AK47 har sau biyu sakamakon rikin cikin gida a unguwar Dago da ke Nyalenda, a gundumar Kisumu na gabas.

Yar sandan mai suna "APC Maureen" ta harbi mijinta ne da bindiga domin ya ba mai yi masu aikin gida kudin kasar Kenya  Ksh50 domin ta saye abinci ta ci ba tare da izinin matarsa ba, kuma wai bai dauki wayarta ba lokacin da ta kira shi.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne lokacin da mijin ke zaune yana kallon Talabijin, kuma ya sami raunuka a gefen kai wajen kunnensa daga gefen giransa. Shi kansa mijin ma'aikacin lafiya ne a garin Kisumu.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabariPrevious Post Next Post