Zawarcin da Tottenham take yi na dan wasan Southampton
dan kasar Denmark Pierre-Emile Hojbjerg, mai shekara 24, ya jefa dan
wasan Ingila Harry Winks, mai shekara 24, cikin halin rashin tabbas a
kungiyar. (Sunday Mirror)
Dan wasan Manchester United
dan kasar Ingila Mason Greenwood, dan shekara 18, zai rika karbar
£40,000 duk mako a sabuwar kwangilarsa a Old Trafford - wata tara bayan
ya sanya hannu kan kwangila a kungiyar. (Sun on Sunday)
Bristol City na son dauko mataimakin kocin Aston Villa John Terry domin ya zama kocinta bayan mutumin da ta yi wa tayi tun da farko Steven Gerrard ya ki amsa tayinta. (Sunday Express)
Arsenal ta shirya biyan £40m domin dauko dan wasan Sporting Lisbon da ke buga gasar 'yan kasa da shekara 17 a Portugal Joelson Fernandes, dan shekara 17, wanda Barcelona da Juventus suke zawarcinsa. (A Bola - in Portuguese)
Har yanzu Chelsea ba ta yanke shawarar dauko Henderson ba. (Sunday Express)
Shugaban Leeds Angus
Kinnear ya ce a makon gobe masu kungiyar za su gana da kocinta Marcelo
Bielsa domin tattaunawa kan sabon kwantaragi da kuma batun musayar 'yan
kwallo don su tunkari gasar Firimiya mai zuwa. (Sunday Express)
Zenit St Petersburg za ta biya £9m don dauko dan waan Liverpool Dejan Lovren, mai shekara 31, sai dai da alama Liverpool na son a biya ta kimanin £15m kan dan wasan na Croatia. (Mail on Sunday)
Villarreal ta
tabbatar da cewa Santi Cazorla ba zai tsawaita zamansa a kungiyar ba, a
yayin da ake rade radin cewa dan wasan na Sufaniya, mai shekara 35,
zai iya komawa Arsenal a matsayin mai horas da 'yan wasa. (Sunday Mirror)
Borussia Dortmund ta sanya farashin £15m kan Jadon Sancho, mai shekara 20, amma dan wasan na Ingila, wanda ake hasashen zai tafi Manchester United, ya ki bayyana cewa zai bar kungiyar ta Jamus. (Sunday Express)
Manchester City tana tattaunawa da kungiyar Brazil Gremio domin dauko dan wasanta na tsakiya dan shekara 17 Diego Rosa a kan £4.5m. (Mail on Sunday).
Source: BBC
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/