Shugaban
Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi wa Ministan harkokin wajen ƙasar
Geoffrey Onyeama addu'ar samun sauƙi, bayan ya kamu da cutar korona.
A
wata sanarwa da mai magana da yawunsa Garba Shehu ya fitar, shugaban ya
bayyana Mista Geoffrey a matsayin wani babban ginshiƙi a mulkinsa, kuma
ya yaba masa kan irin ƙoƙarin da yake yi wurin daƙile yaɗuwar korona.
Mista Onyeama dai na ɗaya daga cikin 'yan kwamitin da shugaban ƙasar ya kafa domin yaƙar cutar korona.
A ranar Lahadi ne dai ministan ya bayyana cewa ya kamu da cutar korona
Ministan
ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter inda ya ce an tabbatar da ya
kamu da cutar bayan an yi masa gwajin cutar karo na huÉ—u.
A saƙon da ya wallafa, ministan ya ce a yanzu haka ya kama hanyarsa ta zuwa wurin killace masu ɗauke da cutar.
Ministan ya zama shi ne farko da ya kamu da cutar korona a jerin ministocin Najeriya.
A
watan Afrilun wannan shekara ne cutar ta yi sanadin mutuwar Malam Abba
Kyari, wanda kafin rasuwarsa shi ne babban hadimin shugaban Najeriya
kuma aboki na ƙut da ƙut ga Geoffrey Onyeama.
Akwai da dama daga cikin 'yan siyasa a Najeriya da cutar ta kama suka warke wasu kuma suka mutu.
Cikin
waÉ—anda suka warke sun haÉ—a da Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai da na
Bauchi Bala Muhammad da Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde.
WaÉ—anda
cutar ta yi ajalinsu kuwa sun haÉ—a da Tsohon Gwamnan Oyo Abiola Ajimobi
da Tsohon Darakta a kamfanin NNPC Engr Sulaiman Achimugu da kuma
Mataimakin Shugaban Jam'iyyar APC reshen Arewa maso Yamma, Inuwa
Abdulkadir.
Sama
da mutum 36,000 cutar korona ta kama a Najeriya, kusan mutum 15,000
suka warke inda kuma kusan mutum 800 suka mutu, kamar yadda hukumar da
ke daƙile cutuka masu yaɗuwa taƙasar NCDC ta bayyana.
Source: BBC
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/