Tabbas an bamu wani kason aikin N-Power mu baiwa mutanen mu - Dan majalisar tarayya

A baya dai kakakin majalisar Dattijai, Sanata Ahmad Lawal ya karyata cewa an basu wani kaso na daukar aikin N-Power..

Saidai shugaban kwamitin dake kula da bangaren rage radadi Talauci na majalisar Wakilai, Abdullahi Balarabe Salaame ya bayyana cewa an ware musu wani kaso na aikin N-Power.

Yace an baiwa ‘yan Majalisar wani kaso na aikinne saboda yanda a baya suka ga yanda ake kashin dankali wajan samun aikin yanda zaka ga wani bangarene kawai na kasarnan ke amfana da abin.Yace ba duka guraben aikin aka basu ba, wani kaso ne daga ciki.

Ya bayyana hakane a hirar da yayi da BBC. Da aka tambayeshi ko ba zasu yi amfani da wannan dama wajan cimma manufofinsu na siyasa ba? Sai yace ai shima shugaba Buhari da ya fito da tsarin Manufofin siyasarsane yake cimmawa dashi.

Yace sun wa mutane alkawurra lokacin da suke kamfe dan haka wannan abu na daya daga cikin amfanuwar da zasuwa mutanensu.

Hutudole


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari



إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN