Sojoji sun kona gidaje da makaranta a wani garin jihar Taraba

An zargi Jami'an Sojojin Najeriya na atisayen Operation Whirl Stroke da kona gidaje da makaranta a garin Peva, karamar hukumar Takum, a jihar Taraba.

Jaridar Punch ta samu hira da mazauna garin inda suka bayyana cewa mutan gari sun tsere yayinda Sojojin suka far ma garin suna kona muhallan jama'a.

Nathan Tyozaenda ya bayyana maneman labaran Punch ta wayar tarho cewa an kona makaranta mallakin Paul Gaza, da safiyar Asabar, 18 ga watan Yuli, 2020.


Tyozenda ya ce Sojojin atisayen Operation Whirl Stroke sun babbaka gidajen shugaban kasuwar doyar Peva, Mr. Orhemba, Mr. Iermber Vaatyough, da Prince Iordye Gaza.

Shugaban al'ummar kabilar Tibi na karamar hukumar Takum, Hon. Peter Suleagbough, ya yi Alla-wadai da irin wadannan hare-hare da lalata dukiyan al'umma.Ya kara da cewa kwanakin baya Sojoji sun aikata irin haka a kauyen Gberifan da Tse-Iorver.4Yace:

"Idan suna neman yan ta'adda kam ar yadda suke ikirari, me zai sa su kona dukiyar mutane?" "Menene alakar makarantar kudi, gidajen mutane da yan ta'adda."

"Kamata yayi Sojoji su rika damke yan ta'addan da suke nema ba kona dukitar mutane ba."

Amma yayinda aka tuntubi kwamandan Operation Whirl Stroke, Manjo Janar Adeyemi Yekini, ya ce ba zai ywu Sojoji haka kawai su kona gidajen mutane ba.

Yace: "Hukumar Sojin Najeriya mai hankali ce da ke aikata abubuwanta bisa rahoto mai inganci kuma ba za a kona dukiyar mutane haka kawai ba."

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN