• Labaran yau


  Yadda Bam ya hallaka yara 6 kuma ya jikkata 5 a Malumfashi (Hotuna)

  Akalla yara biyar sun rasa rayukansu yayinda shida sunyi mumunan jikkata bayan Bam ya tashi da su a kauyen 'Yar mama dake karamar hukumar Malumfashi a jihar Katsina.

  Hukumar yan sandan jihar sun ce yara biyar suka mutu amma masu idanuwan shaida sun bayyana cewa yara 6 ne. Wannan abu ya faru ne yau Asabar, 18 ga watan Yuli, 2020.

  Bisa jawabin da kakakin hukumar, Gambo Isha, ya ski, tashin Bam din ya auku ne cikin gonan wani Malam Hussaini Mai Kwai. Ya ce hukumar ta kaddamar da bincike cikin lamarin.

  Gambo Isah ya bayyana cewa yara guda 11 na yankan ciyawa ne don ciyar da dabbobi lokacin da abin ya auku. Yayinda biyar suka mutu kai tsaye lokacin, an garzaya da biyar Asibitin garin Malumfashi domin jinya.

  Source: Legit.ng


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yadda Bam ya hallaka yara 6 kuma ya jikkata 5 a Malumfashi (Hotuna) Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama