Shugaba Buhari yayi bayanin dalilin da yasa aka yiwa kasafin 2020 kwaskwarima

Rahotub Hutudole

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana ce Gwamnatin Tarayya ta yi wa Dokar Kasafin 2020 kwaskwarima ce domin a gaggauta shigar da tsare-tsaren da suka wajaba wajen inganta ayyukan lafiya na gaggawa.

Buhari ya kara da cewa an yi wa dokar kasafin na 2020 kwaskwarima, har saboda bijiro wa al’ummar kasar nan ayyukan da za su rage radadin kuncin da aka shiga saboda bullar cutar Coronavirus.

Buhari ya yi wannan jawabi a Abuja, lokacin da ya sanya hannu a kan sabuwar dokar kasafin, bayan da Majalisa ta amince kuma ta tura masa dokar, domin sa mata hannun tabbatar da ita zama doka.
A cikin jawabin da ya yi, Buhari ya tunatar da cewa, ya sa wa dokar kasafin 2020 hannu tun a ranar 17 Ga Dusamba, 2019.
“To sai dai kuma bullar annobar Coronavirus ta karya farashin danyen mai a duniya, inda tun yana ganga daya dala 72.20 cikin Janairu, 2020 har sai da farashin ya zube kasa da dala 20 a cikin Afrilu 2020. Tun daga lokacin har zuwa yau, ko ya yi tsalle sama, sai dai ya yi faduwar-faduwar-‘yan-bori domin ba ya wuce dala 40 duk ganga daya.

Ya ce amma kwaskwarimar da aka yi wa kasafin a yanzu, da kuma Shirin Cika Cikin Tattalin Arziki da naira tiriliyan 2.3 da gwamnati ta bijiro da shi, zai sa jikin ‘yan Najeriya ba zai nuna jigata da komatar kuncin tattalin arziki ba.”

Daga nan ya umarci dukkan Ministoci da ma’aikatu da hukumomin da ke karkashin su, su maida hankali sosai wajen aiwatar da manyan ayyukan bunkasa kasa.

Sannan kuma su rika tuntubar Ma’aikatar Harkokin Kudade, Kasafi da Tsare-tsare domin cim ma komai a bisa yadda kasafin 2020 ya zayyana.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabariPrevious Post Next Post