Kasar Sudan ta dage dokar hana shan barasa ko yin ridda ga wadanda ba Musulmi ba

A karon farko, a fiye da shekara 30, kasar Sudan za ta dage dokar hana wadanda ba Musulmi ba shan barasa da kuma dokar kisa idan Musulmi ya bar addinin Musulunci (Ridda) zuwa wani addini a cewar Ministan shari'a na kasar.

Wadannan sauye sauye na zuwa ne bayan kawar da mulkin shugaba Omar Al-bashir wanda ya jagoranci kasar Sudan har tsawon shekara kusan 30.

"Yanzu kasar Sudan za ta bar wadanda ba Musulmi ba su sha barasa matukar yin haka ba  zai takura ko ya tayar da hankalin jama'a, ko a yi hakan a bainar jama'a ba" a cewar Ministan shari'a na kasar Nasredeen Abdulbari lokacin wani tattaunawa a gidan Talabijin na kasar ranar Asabar.

"Ba wanda ke da ikon kiran wani Kafiri saboda baya cikin addininsa, wannan yana jawo tashin hankali da matsalar tsaro a cikin al'umma kuma yakan kai ga daukan fansa da ke haddasa kashe kashe a cikin al'umma" Inji Ministan shari'a Nasredeen.

Akan yanke hukunci kisa matukar Musulmi ya canja addini daga Musulunci zuwa wani addini a inda Musulmi ke da rinjaye.

Omar Al-bashir ya jaddada dokar a zamanin mulkinsa a kasar Sudan bayan ya dare Karagar mulki a 1989 ta hanyar juyin mulkin soja

Akwai mabiya Darikun addinin Kirista na Copts, Catholics, Anglican da sauransu a kasar Sudan, amma sakamakon tsauri da tursasawa a zamanin mulkin Al-bashir ya sa suka noke.

A 2014, an yaanke ma wata mata hukuncin kisa bayan ta canja sheka daga addinin Musulunci zuwa na Kirista, lamari da ya jawo cece kuce tare da alla wadai daga kasashen Duniya.

Bayan matsin lamba daga sassan Duniya, Sudan ta dakatar da hukunci kuma ta saki matar, daga bisani ta gudu zuwa kasar Amurka.

DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabariPrevious Post Next Post