Kampanin hakar mai na Najeriya NNPC ta yi wani babban sauye sauye a ma'aikatar wanda ya shafi wasu manyan Darakroci.
Kakakin kampanin na kasa Kennie Obateru ya sanar da haka ranar Lahadi a birnin Abuja.
Ya ce NNPC ta dauki wannan mataki ne bisa tsarin Next-Level na shugaba Muhammadu Buhari domin tabbatar da gaskiya da adalci wajen tafiyar da aiki.
Wadanda sauye sauyen wajen aikin ya shafa sun hada da manyan Daraktoci:
Adokiye Tombomieye na sashen Crude Oil Marketing Division (COMD) an mayar da shi COO. Sauran su ne
1. Mohammed Abdulkabir Ahmed, babban Darakta na Nigerian Gas Marketing Company (NGMC), yanzu shi ne COO, Corporate Services.
2. Adeyemi Adetunji, COO na Upstream yanzu shi ne shugaban Ventures and Business Development Directorate.
3. Billy Okoye, MD na NNPC Retail Limited yanzu shi ne Group General Manager, Crude Oil Marketing Division.
4. Elizabeth Aliyuda, GM na Sales and Marketing NNPC Retail Limited, yanzu ita ce MD na wannan sashe na kampanin
5. Usman Farouk, babban Darakta na Asset Management and Technical Services na NGMCyanzu shi ne MD na wannan Kampani.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Tags:
LABARI