Da dumi dumi: Yadda aka hana mataimakin gwamnan Oyo shiga wajen addu'an takwas na Ajemobi

An sha ‘yar dirama a ranar Lahadi a Oluyole, gidan marigayi tsohon gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi, lokacin da aka hana mataimakin gwamnan jihar Rauf Olaniyan shiga wajen addu’an kwana takwas na rasuwarsa, wanda aka gudanar a harabar gidansa.

Iyalan mariayin sun sanar da cewar taron addu’an zai zama na takaitattun jama'a, inda suka bukaci jama’a da su kalla ta yanar gizo kamar a Zoom, YouTube da Facebook. Olaniyan ya isa gidan da misalin 11:20 na safe a ayarin motoci biyar.

Amma da ya kofar da zai shigar dashi hanyar gidan Ajimobi, sai yan sanda da sauran jamián tsaro suka dakatar da ayarin motocin. Suka ce lallai sai dai motai mataimakin gwamnan nekadai za a bari ya shiga unguwar don halartan taron.

Da fari jami’an tsaron gwamnan sun ki amincewa da shawarar amma a lokacin da hayaniyarsu ya yi yawa, sai wani babban dan sanda ya sanya baki sannan suka amince cewa motar mataimakin gwamnan kadai ya shiga. Amma da suka isa gidan Ajimobi, sai suka kara tarar da kofar a rufe.

Hadiman mataimakin gwamnan sun gabatar da ubangidansu amma aka sanar masu da cewar an rufe kofar, jaridar The Nation ta ruwaito. Sannan cewa uwargidar Ajimobi ce ke rike da makullin. Olaniyan ya jira inda yake tunanin za a magance lamarin kan lokaci. Bayan ya jira tsawon mintuna 15 ba tare da wani ci gaba ba sai Olaniyan ya bar gidan

Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabariPrevious Post Next Post