Rundunar sojin sama na Najeriya ta fitar da sanarwa da ta musanta cewa da kafofin labarai suka yi cewa shugaban mayakan sama na Najeriya Air Vice Marshal Sadiq Abubakar ya ce rundunar za ta kakkabe yan kungiyar boko haram kafin karshen wannan shekara ta 2020.
Babban jami'in rundunar kan hulda da jama'a Air Commodore Ibikunle Daramola ya sanar da haka ranar Lahadi biyar ga watan Juli. Ya ce sanarwar haka ta zo ne bisa tsari domin kawar da yadda rahotanni suke alakanta karshen boko haram da shugaban mayakan sama bisa kayyadadden lokaci wanda ba haka zancen yake ba.
Ya kara da cewa shugaban mayakan sama na Najeriya AVM Sadiq Abubakar bai kayyade wa'adin kakkabe boko haram ba.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari