Mata, yara da yan uwanka sun fi kuntata maka bisa manesantanka - Imam Muhktar

Limamin babban Masallacin Juma'a na jihar Kebbi Imam Muhktar Abdullahi ( Walin Gwandu) ya yi nasiha ga al'umma Musulmi su sa ido kuma su kula da tarbiyyan 'ya'yansu da iyalansu domin samar da ingantaccen al'umma masu ladabi da dabiyayya  don samun wanzuwar zaman lafiya da ci gaba.

Imam Muhktar ya yi wannan bayani ne a daya daga cikin Huduban Juma'a da ya saba gabatarwa a Masallacin ( Centralm Mosque) da ke garin Birnin kebbi.

Ya ce " Allah ,adaukakin Sarki ya yi tarbihi mai muhimmanci kwarai ga rayuwarmu a inda yake cewa hakika daga cikin ku, matan ku da yayan ku, akwai makiya gareku, ku yi hattara da su. Kuma idan mun lura, tabbas mutane sun fi son 'ya'yansu da matansu, da abokansu da sauransu.

To amma in mutum ya tsaya ya kalli rayuwa da kyau, sai ka iske mafi yawan masu cuta maka tsakanin yan uwa ne, mata da diyanka da makusantan ka sun fi cuta maka fiye da wadanda suke nesa da mutum, musamman lokacin da aka sami rashin tarbiyya tsakaninsu, babu abin da ba za su iya aikatawa ba,

Yan uwa suna kashe yan uwa, yan uwa sun sha kulla wa yan uwa sharri, kowane idan ra'yinku ya banbanta da shi ba abin da ba zai iya aikatawa ba. Saboda haka sakaci daga sharrin makusanci ba karamin hadari bane. Wasa da tarbiya da muke yi su suka jawo haka, suna sa samari suna ta'addanci kuma su zama makiya ga babanninsu.

Da babanninsu sun tsayu,  bisa ga hanyar da ta dace, suka san nauyi da aka aza masu suka dauke shi suka yi aiki da tabbatar da shi,. Muna rokon Allah ya yi mana afuwa, Allah ka bamu, matan mu da zuri;armu abin da zai sa mu farin ciki, ya sa mana jagorori masu imani, ya bamu kyakyawar rayuwa a Duniya da Lahira ya kare mu daga azabar Wuta". Inji Imam Muhktar.

   ".

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN