A ranar Alhamis din nan ne kungiyar kwadago ta Najeriya,
NLC, ta yi watsi da sabon farashin man Fetur da Hukumar dake kayyade
farashin Albarkatin mai ta kasa, PPPRA ta fitar, ta kuma bukaci da a
mayar dashi farashin da, tana mai cewa sabon farashin, a tsakiyan
annobar cutar korona, zai kashe kasuwanci da kuma kara talauci a fadin
kasar.
NLC, a cikin wata sanarwa daga shugaban ta, Ayuba Wabba,
ta yi ikirarin cewa hauhawar farashin man, Premium Motor spirit, wacce
aka fi sani da ‘man fetur’ daga Naira 121 zuwa Naira 143.80 a daidai
lokacin da yan Najeriya da yan kasuwa ke kokawa da mummunan sakamakon da
annobar korona ta haifar, shine maifi girman rashin kulawa daga
gwamnati.
Sanarwar ta bayar da hujjar cewa “PPPRA ta sabawa kanta
lokacin da ta ce sabon farashin da aka bayyana a matsayin” na shawara
“an tsara shi ne don tsara samfurin da aka ce gwamnati ta tsara.
Hutudole
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari