Gwamna Masari ya jagoranci Katsinawa wajan addu’ar neman taimakon Allah game da yan bindiga

A ranar Alhamis ne gwamna Aminu Masari ya jagoranci mazauna jihar Katsina da su nemi taimakon Allah wajen fada da yan fashi da makami, satar mutane da satar shanu da ke addabar jihar.

Taron addu’o’in na kwanaki uku wanda ya fara da misalin karfe 10 na safe ya kwashe tsawon awanni uku a Masallacin Juma’a da ke babban birnin jihar, inda sama da mutane dari uku galibi mahaddatan Alkur’ani mai girma suka mamaye zaman.

A cewar masu addu’ar ta nuna damuwar gaba daya al’ummomin a fadin jihar don kawo karshen wannan matsalar.

Sun kara bayyana shi a matsayin wani abu ne da zai sanya jami’an tsaro a kasa su fahimci cewa membobin jama’a suna tare da su a kokarinsu na fatattakar masu ayyukan ta’addancin.

Mataimakin gwamnan jihar, Injiniya Mannir Yakubu, kwamishinan labarai, al’adu da al’amuran gida, jihar Katsina, Alhaji Abdulkareem Yahayya Sirika, mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin tsaro, Ibrahim Ahmad Katsina, da Sakatare na dindindin, Ma’aikatar Addini ta Katsina, Lauya Mohammed Lawal Matazu suna daga cikin manyan bakin da suka halarci taron addu’ar.

Idan za a iya tunawa, Rundunar Sojin Najeriya a ranar Laraba ta ba da tabbaci ga ‘yan kasar bisa kudurin ta na ci gaba da aiki tare da sauran hukumomin tsaro don inganta zaman lafiya da tsaro a duk fadin kasar.

Wannan tabbacin ya zo ne a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ga sojoji don dakile wasu yan bindiga da ke addabar yankin Arewa maso yammacin kasar.

Babban hafsan sojojin, Laftanar Janar Tukur Buratai ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a Faskari, daya daga cikin rundunonin na jihar Katsina yayin bikin ranar sojojin Najeriya ta bana, NADCEL.

Hutudole


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabariPrevious Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN