Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya ba da sanarwar sayar da takin zamani a tallafin kudi na Naira 4,000 a kowace jaka.
Tambuwal, yayin da yake ba da sanarwar sayarwa da
rarrabawa a shagon sayar da kayan aikin gona, a Kasarawa, a karamar
hukumar Wamakko, ya ce manufar ita ce bunkasa harkar noma, rage talauci
da samar da ayyukan yi a jihar.
Gwamnan ya ba da sanarwar cewa jaka
daya ta kilo 50 na nitro, phosphorus, potassium wanda aka samo daga
Gwamnatin Tarayya akan farashin Naira 4,500 zai sayar a kan Naira 4,000,
yayin da Urea wanda aka samo akan Naira 9,800 a kasuwa za’a siyar akan
Naira 5,000 akan jaka.
Hutudole
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari