Ko Ibrahim Magu mai gaskiya ne? duba abin da Shehu Sani ya ce

 Legit

A daidai lokacin da tsohon shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya ke tsare, bayanai sun fara fitowa a game da irin rikon da ya yi a lokacin da ya ke kan kujera. Shehu Sani ya bayyana cewa Ibrahim Magu wanda wasu ke ganin cewa ta shi ta zo a karshe a yanzu, ya rika amfani da wasu miyagu da ake kira ‘Yaran Magu’ a lokacin da ya ke kan kujera.

Tsohon sanatan ya ce jami'an da ke cikin wannan gungu na ‘Yaran Magu’ ko yaran oga da aka kafa shekarun baya, duk sun fito ne daga wani bangare guda na kasar nan. Ibrahim Magu mai shekaru 58 a Duniya asalinsa mutumin garin Maiduguri ne a jihar Borno.

Ya na cikin wadanda su ka taimakawa Nuhu Ribadu a lokacin da ya ke rike da EFCC. Sanata Shehu Sani ko da ba a ji mutuwar sarki a bakinsa ba, ya nuna cewa sauran ma’aikatan EFCC su na da labarin aikin da wadannan yara da Magu ya kafa su ka rika yi. “Abin da za ka yi kurum shi ne ka tambayi sauran jami’an hukumar masu gaskiya su fada maka abin da su ke yi.” Sani ya bayyana wannan ne a shafinsa na Twitter a ranar Laraba.

Ba Sani kadai ya ke zargin Ibrahim Magu da ba daidai wajen aiki ba. Olusegun Adeniyi wanda ya yi aiki da tsohon shugaban kasa Ummaru ‘Yar’adua bai yi kalamai masu dadi game da Magu ba. Olusegun Adeniyi ya ce tsohon shugaban hukumar ta EFCC ya rika wulakanta wasu manya da ake ji da su a kasar nan a lokacin da ya ke ofis, daga cikinsu har da tsohon shugaban kasa.

A rahoton da DSS ta fitar game da Magu a 2016, ta zarge shi da yin karfa-karfa kamar ana mulkin soji. Ana kuma zargin cewa shi kan sa mukaddashin shugaban na EFCC ya na da kashi a gindi. Hukumar DSS ta ce Magu ya na aiki ne da jita-jita, malaman tsibbu, tare da kuma shigar da siyasa wajen aikinsa.

A dalilin wannan majalisa ta ki tantance shi har sau biyu. A baya an zargi Magu da rashin sanin kan aiki, da cin mutuncin hukumomi ma’aikatun gwamnati domin wata manufarsa, wanda hakan ya batawa EFCC suna a idon Duniya.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabariPrevious Post Next Post