Ka sa Wakili shugabantar EFCC don aiki da cikawa, yan arewa sun shawarci Buhari

Legit

Da yawan 'yan Najeriya, musamman 'yan arewa, da ke amfani da dandalin sada zumunta sun shawarci shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya nada tsohon kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, Muhammed Wakili, a matsayin mukaddashin shugaban hukumar EFCC. Jama'a sun fara wannan kirane ranar Laraba a shafin Tuwita bayan sanar da cewa shugaban kasa ya dakatar da mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, a ranar Talata.

A ranar Litinin ne wani kwamitin bincike da shugaba Buhari ya kafa ya gayyaci Magu zuwa fadar shugaban kasa domin ya amsa tambayoyi a kan wasu zarge - zarge ma su nauyi da ministan shari'a, Abubakar Malami, ya yi a kansa. Ganin cewa ana ta yada jita - jitar cewa an nada wanda zai maye gurbin Magu kafin daga baya fadar shugaban kasa ta karyata, wasu 'yan Najeriya sun ce kamata ya yi shugaba Buhari ya nada wani mutum mai gaskiya daga arewa.

Wasu dumbin ma su amfani da manhajar Tuwita sun shawarci Buhari, ta hanyar ambaton shafinsa, @MBuhari a kan ya duba yiwuwar nada Wakili a matsayin sabon mukaddashin shugaban hukumar EFCC.

A yayin da wani mai suna Victor Ita James ya shawarci ''shugaba Buhari da majalisa su duba wani mutum mai kima da gaskiya daga wani yankin bayan arewa domin nada shi a matsayin shugaban EFCC. "Idan kuma ba zai nada wani mutum ba sai daga arewa, mun yarda da nagarta da gaskiyar Muhammed Wakili.

Kazalika, wani mai suna Famous Anfield ya bayyana cewa; "ina goyon bayan tsohon kwamishina Muhammed Wakili (Singham) domin ya maye gurbin Ibrahim Magu a matsayin shugaban EFCC. Ya na da dukkan nagartar da ake bukata."

Wani ma'abocin amfani da dandalin sada zumunta ya ce; "na yi aiki tare da tsohon kwamishina Muhammed Wakil (AKA Singham) lokacin ya na jagorantar sashen gudanarwa na ofishin hukumar EFCC da ke Kano."

"Na yaba sosai da nagartarsa, na yi koyi da shi har na samu gagarumar nasara a matsayina na shugaban kungiyar yaki da cin hanci ta matasa 'yan hidimar kasa (NYSC) a Kano." Wakili, tsohon kwamishinan 'yan sanda, ya samu lakabin ''Singham'' saboda jarumta, gaskiya, da jajircewarsa a bangaren aiki, musamman yaki da shan miyagun kwayoyi."

Singham ya taba kama mataimakin gwamnan jihar Kano, Dakta Nasiru Gawuna, da kwamishinan kananan hukumomi, Murtala Garo, bayan sun kawo hargitsi da tayar da kura a wajen tattara sakamakon zaben gwamnan Kano a watan Maris, 2019. Har yanzu 'yan Najeriya da dama su na yabon Singham saboda jarumta da gaskiyarsa duk da ya yi ritaya daga aiki.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabariPrevious Post Next Post