Da dumi dumi: An kama wani shugaban jam'iyan APC yana yi wa yara yan mata 2 fyade

Rundunar yansandan jihar Nassarawa ta kama wani dan siyasa mai suna Christopher Ogah bayan an yi zargin kama shi yana yi wa yara yan mata biyu fyade a gidansa da ke karamar hukumar Obi a jihar ta Nassarawa.

An kama Christopher wanda shi ne Ciyaman na jam'iyar APC a Mazabar Obi dumu dumu yana yi wa yaran yan shekara 12 da 13 fyade a gidansa.

Daily Trust ta ruwaito cewa Christopher ya rudi yaran ne suka shiga dakinsa bayan sun je diban ruwa a gidansa.

Shugaban karamar hukumar Obi  Alhaji Mohammad Oyimoga Oyigye ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce da kansa ne ya ceci rayuwar Christopher bayan fusatattun matasa sun afka masa da duka.

Ya ce an mika wanda ake tuhumar ga yansanda kuma suka garzaya zuwa Lafiya babban birnin jihar da shi bisa dalilan tsaro.

Haka zalika Kwamishinan yansandan jihara Nassarawa Mr Bola Longe ya tabbatar da faruwar lamarin.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabariPrevious Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN