Wani masanin ilimin hada magunguna mai shekaru 34, ya shake matarsa inda ta sheka lahira saboda ya samu lokacin shakatawa da abokin luwadinsa.
Kafin mutuwar matar mai suna Jessica Patel, an samu shaidun cin zarafi don tayi ikirarin cewa ya taba banketa da mota. Patel ya mayar da Jessica yankin Middlesbrough daga Halifax, yammacin Yorkshire, wanda 'yan uwanta suka ce don ya killace ta ne.
Mitesh Patel, wanda shima masanin ilimin hada magunguna ne, ya kwashe shekaru 5 yana tsara yadda zai kashe matarsa don ya yi amfani da kwantaccen cikinta don ya fara rayuwa da abokin luwadin shi wanda ya hadu da shi a manhajar Grindr.
Ya kara da tsara yadda zai karbe pam miliyan 2 na inshorar rayuwarta. Ya ce wani ne ya shiga gidansu inda ya kashe mishi mata. Miyagun tsare-tsarensa sun fallasa ne sakamakon wata manhajar kiwon lafiya da ke wayarta da ta nade dukkan abinda ya faru bayan da ya kashe matar.
An yankewa Mitesh hukuncin shekaru 30 bayan alkalin ya kwashe sa'o'i biyu da mintuna 50 yana yanke hukuncin kisan kai da yayi. 'Yan uwan Jessica sun matukar razana da mutuwarta.
"Aljanna ta samu bakuwa, amma duniya tayi babban rashi. Jessica mutum ce da ba a samun irinta. Kyakkyawa ce ciki da waje. "Tana da zuciya mai matukar kyau tare da karamci ga dukkan wadanda ta hadu da su. Ita ce diyar farko kuma ta kawo matukar farin ciki ga iyalan," suka ce.
A wani labari na daban, Wani matashi mai shekaru 29 ta sheka lahira bayan sanar da abokinsa makuden kudin da ke asusun bankinsa, wanda yayansa da ke kasar Afrika ta Kudu ya turo masa don kammala ginin gidansa a Najeriya.
Moses ya halaka abokinsa Abuchi Wisdom Nwachukwu har lahira, bayan sanar da shi da yayi akwai Naira miliyan 13 a asusun bankinsa. Nwachukwu dan asalin karamar hukumar Isiala-Mbano ne da ke jihar Imo.
Ana zargin an kashesa ne a ranar 7 ga watan Janairun 2020 a yayin da yake aikin dare a wani gidan ruwa da ke Auchi a jihar Edo. Daga nan wanda ake zargin ya dauke waya tare da ATM na mamacin.
Moses ya cire kan abokinsa Nwachukwu daga gangar jikinsa ta yadda ba za a ganeshi ba, kuma ya yasar da gangar jikin da babu kai a wani daji da ke kusa da kamfanin.
Bayan yasar da gawar Nwachukwu, Moses ya dauke wayarsa tare da ATM din shi, wanda ya kai wa wasu masu damfarar yanar gizo inda suka kwashe N2.2 miliyan daga asusun bankinsa.
Source: Legit
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/ L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/