• Labaran yau


  Dashen Gaɓar Ƙugu da ababe 6 da ya kamata ka sani

  Gaɓar ƙugu na daga cikin gaɓɓan da aka fi yi musu dashen gaɓa a cikin gaɓɓan jiki.

  Gaɓar ƙugu ta haɗa da 'ƙwallon ƙashin cinya', wato kan ƙashin cinya da 'kwarmin ƙugu', wato ramin ƙugu da kan ƙashin cinya ke ciki.

  Gabar ƙugu na lalacewa yayin da 'ƙwallon ƙashin cinya' da 'kwarmin ƙugu' suka sami karaya ko suka lalace sakamakon matsaloli kamar:

  1. Karaya daga bugu, faɗowa ko haɗarin ababen hawa
  2. Lalacewar ƙasusuwan saboda ciwon sikila, ciwon daji/kansa
  3. Amosanin gaɓar ƙugu, wato zaizayewar guruguntsin gaɓar ƙugu
  4. Lalacewar ƙasusuwan sakamakon shigar ƙwayoyin cuta gaɓar, da dai sauransu.

  Waɗannan matsaloli na tilasta yin dashen gaɓar don ceto aikinta. Likitan tiyatar ƙashi ne zai jagoranci yin wannan dashe bayan lura da duk wani abu da ka-je-ya-zo.
  Abubuwan da ke biyo bayan aikin sun haɗa da:

  1. Ciwo daga gaɓar ƙugun zuwa ƙafa
  2. Kumburi
  3. Nauyin ƙafar
  4. Rauni/rashin ƙwarin tsokokin ƙafar
  5. Tabon yankan tiyata
  6. Riƙewar gaɓoɓin ƙugu, gwiwar ƙafa

  Bayan likitan ƙashi ya gama aikinsa, za a gayyaci likitan fisiyo don ci gaba da kula da mara lafiyar domin a shawo kan matsalolin da aka ambata har aikin gaɓar yai kyau, ƙafar tai ƙwari mutum ya dawo tafiya ba tare da wata matsala ba.

  Muhimman aikin likitan fisiyo a dashen gaɓar ƙugu sune: rage ciwo, rage kumburi, bunƙasa aikin gaɓar, bunƙasa ƙwarin tsokokin ƙafar, koya tafiya, da koya ayyukan yau da kullum ba tare da jin ciwo ba ko kuma lalacewar aikin.

  #TotalHipReplacement

  Source: Physio Hausa

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Dashen Gaɓar Ƙugu da ababe 6 da ya kamata ka sani Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama