Yan mata biyu sun kasa tafiya bayan an gama aiwatar masu da hukuncin bulala sakamakon
kama su da laifin cudani da maza ba tare da aure ba a kasar Indonesia wacce ta ke bin tsarin shari'ar Musulunci.
Tun a shekarar bara ne aka kama wasu maza da mata guda shida bayan
yansanda sun kai samame a wani Hotel a yankin Banda Aceh na kasar
Indonesia.
Bayan sun shafe watanni a Kurkuku, sai a ranar Litinin aka zartar masu da hukuncin bulala a bainar jama'a.
Kowace daga cikin yan matan ta sha bulala 25 domin sun yi cudani da maza a dakin Hotel.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari